Site icon Muryar 'Yanci – Labaru, Siyasa, Tsaro, Lafiya, Ilimi…

Ambaliyar Ruwa Ya Raba Mutum Miliyan Guda Da Muhallinsu – Ma’aikatar Jin Kai


Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Ma’aikatar jin kai ta fitar da sabbin alkaluman na yawan adadin mutanen da suka mutu sakamakon ambaliyar ruwa a kasar.

Ministar ma’aikatar Sadiya Farouk, ta ce yawan mutanen sun kai 603.

Sannan kuma an kiyasta cewa mutane fiye da miliyan daya da dubu 300 ne suka rasa muhallansu sakamakon ambaliya ruwa a fadin kasar.

Ministar ta ce,” Akwai wadanda suka samu raunuka sakamakon ambaliyar wanda yawansu ya kai dubu 2,407,, sannan kuma akwai gidaje dubu 121, 318 da ambaliyar ta shafa.”

Sadiya Farouk, ta ce akwai kuma gidaje  fiye da dubu 82 da gaba Daya suka tashi daga aiki.

Ministar ma’aikatar jin kan ta ce akwai gonaki da dama da ambaliyar ta lalata a fadin Najeriyar.

Sadiya Farouk, ta ce sakamakon abin da ya faru a bana, a yanzu akwai matakan da ya kamata a dauka na kaucewa samun irin wannan mummunar asara, kamar kwashe mutanen da ke zaune a gabar ruwa.

Ta ce saboda gudun sake afkuwar wannan iftila’i sun fadakar da mutane kana sun zauna da gwamnonin jihohi in da muka sanar da su illar ambaliyar ruwa don su dauki matakan da suka dace.

Ministar ta kuma yi gargadin cewa za a ci gaba da fuskantar irin wannan masifar ambaliyar ruwan a yankin kudancin Najeriya har nan da watan Nuwamba.

A bana dai an samu ambaliyar ruwa da dama a jihohin Najeriya ciki kuwa har da Kano da Jigawa da Bauchi da Lagos da sauransu. 

Exit mobile version