Ambaliyar Ruwa Ya Lakume Rayuka 134 A Jíhar Jigawa

Labarin dake shigo mana daga Dutse babban birnin Jihar Jigawa na bayyana cewar Gwamnatin jihar ta ce akalla mutum 134 ne suka mutu, yayin da aka yi hasarar dukiya ta kusan naira tiriliyan 1.5, sakamakon ambaliya ruwa da jihar ke fuskanta.

An ruwaito mataimakin gwamnan jihar Alhaji Umar Namadi, na bayyana hakan ranar Asabar, lokacin da ya karbi bakuncin shugaban Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF mai kula da jihohin Kano, da Katsina, da jigawa Rahman Rihub Mahmud Fara,

Ya kara da cewa ruwan na ci gaba da bin yankin gabashin jihar, inda ya ce kananan hukumomin Birninwa, da Kirikasamma na cikin hatsari.

Labarai Makamanta