Ambaliyar Ruwa Na Neman Shafe Birnin Legas

Yayin da mazauna Legas ke ci gaba da fuskantar matsalar ambaliyar ruwa kowacce shekara, musamman a watannin Maris zuwa Nuwamba, a ‘yan shekarun nan yankin na fama da mummunan matsalar ambaliyar ruwa.

Wannan na zuwa ne dai-dai lokacin da hukumomi a Najeriya ke ci gaba da gargadin aukuwar wata ambaliyar nan da dan lokaci kadan.

Haka zalika masana na ganin cewa birnin na Legas ya fara nutsewa a cikin ruwa, sakamakon matsalar dumamar yanayi.

Tuni gwamnatin Jihar ta sanar da jama’a musamman waɗanda ke maƙwabtaka da bakin ruwa da su yi gaggawar kauracewa yankin domin kaucewa afkawa cikin Iftila’in.

A hannu guda kuma birnin Haɗeja na jihar Jigawa shima yana cikin mawuyacin hali sakamakon matsalar Ambaliyar ruwa da ta addabi yankin, inda jama’ar cikin birnin ke cikin damuwa da tashin hankali gami da fargaba na abin da zai je ya dawo.

Hakazalika wannan Iftila’i na ambaliyar ruwa ya yi ta’adi a Jihar Neja inda ruwan ya lashe maƙabartu da tafiya da tarin gawarwaki a cikin makon da ya gabata a yankin Mariga dake Jihar.

Jihohin Najeriya da dama na fuskantar barazanar faruwar Iftila’in ambaliyar ruwa kamar yadda masana suka faɗi na cewar an jima ba a ga irin wannan Iftila’in a faɗin ƙasar ba a tsawon shekaru.

Labarai Makamanta