Amaechi/El Rufa’i: Ba Ni Da Alaƙa Da Hotunan Da Ake Yaɗawa – El Rufa’i

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya musanta sanin masu hada hotunansa a fosta da sunan kamfen dinsa a matsayin mataimakin shugaban kasa a zaben 2023 dake gabatowa.

Gwamnan ya sanar da hakan ne yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai bayan haduwarsa da mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo a fadar shugaban kasa da ke Abuja, ranar Juma’a.

Gwamnan jihar Kaduna ya ce har Amaechi ya kira amma ya ce shi sam bai san wadanda suka yi ta hada hotunansu a takardu suna mannawa ba.

A cewarsa, “Ina da burin zama gwamnan da yafi kowanne nagarta da aiki, kuma ina yin iyakar kokarina wurin ganin nayi wa jihata ayyuka yadda yakamata, daga yanzu har 2023.

Amma bayan 2023, zan bar komai a hannun Allah. Gwamnan ya kara da bayyana yadda matsalar rashin tsaro da ke jiharsa take ci masa tuwo a kwarya da yadda masu garkuwa da mutane suka kara yawa, yana da burin ganin ya magance wadannan matsalolin tukunna.

Labarai Makamanta