Dan takarar gwamnan jihar Kaduna Sanata Uba Sani mai wakiltar mazabar kaduna ta tsakiya, ya cika alkawari na bayar da gudunmawar naira miliyan 20 ga ‘yan kasuwar da ke yin kasuwanci sassan jihar kaduna, musamman don su sayi shaguna.
Uba Sani ya bayar da wannan gudunmuwar ne, biyo bayan wata ganawar da ya yi da masu ruwa da tsaki da ‘yan kasuwa a watan Satumbar 2022, inda shugaban KMDMC Tamar Nnandul ta shedawa mahalarta taron cewa, za sayar da wasu shaguna don gudanar da kasuwanci.
Sanata Uba Sani a yau, ya cika alkawarin sa kuma mun fara rabar da tallafin ga sama da ‘yan kasuwa 700 da ke a daukacin jihar.
Wasu daga cikin manyan baƙin da suka halarci taron sun hada da, Kantoma kuma kwamishinan na sauya fasalin jihar Kaduna, Darakta Janar na kwamitin yakin neman zaben Sanata Uba Sani, farfesa Sani Bello (Mainan Zazzau) shugaban yan kasuwa na jihar da sauransu.
Bugu da kari, Uba Sani ya kuma kaddamar da wasu shaguna biyu da ke a cibiyyar da ke a kan titin Lagos wato tsohon garejin 7/40 da kuma na titin Ibrahim Taiwo wato tsohon garejin 69.
Gwamnatin jihar Kaduna a karkashin mulkin gwamnan jihar Nasir Ahmed El-rufai ta gyra gurin a karkashin shirinta na sake farfadon da martabar Kaduna.
You must log in to post a comment.