Alkalin Alkalan Najeriya: Tanko Ya Fita Olukayode Ya Shigo

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar an rantsar da Mai shari’a Olukayode Arwoola a matsayin muƙaddashin babban jojin kasar.

Hakan ya biyo bayan murabus da Mai shari’a Ibrahim Tanko Muhammad ya yi, mai shari’a Tanko ya yi murabus ne bisa dalili na rashin lafiya.

Mai shari’a Olukayode Ariwoola shi ne ke bi wa babban jojin Najeriya Mai shari’a Ibrahim Tanko Muhammad baya, kuma tuni ya karbi rantsuwa tare da karɓar ragama a matsayin mukaddasshin babban jojin Najeriya.

An wayi gari da labarin murabus din babban jojin Najeriyar, Mai shari’a Ibrahim Tanko Muhammad, labarin ya ɗauki hankali duba da yadda ya mamaye kafafen yada labaran kasar da dama.

Labarai Makamanta