Alkalai Na Cin Amanar Shari’a A Najeriya – Jega

Rahoton dake shigo mana daga Abuja babban birnin tarayyar Najeriya na bayyana cewar tsohon shugaban hukumar zabe na kasa watau INEC, Farfesa Attahiru Jega yace wasu bara gurbin Alkalai su na cikin masu kawo cikas a kasar nan.

Farfesa Attahiru Jega yana cewa ana sa Alkalan kotu a harkar sauraron korafin zabe ne domin su samu hanyar da za su cika aljihunsu. A cewar babban malamin jami’ar, wasu Alkalan su na saida shari’ar zabe, sai suyi wuf, suyi ritaya daga aiki domin gudun majalisar shari’a ta kasa ta hukunta su.

Farfesa Jega ya yi wannan furucin ne a lokacin da ya gabatar da watta lacca domin tunawa da Owolabi Afuye da kungiyar lauyoyi ta NBA ta shirya a Ibadan, jihar Oyo.

Tsohon shugaban jami’ar ta Bayero da Kano, yace danyen aikin da Alkalai suke yi yana cikin abubuwan da ke haddasa rashin tsaro.

“Wasu manyan lauyoyi sun yi kazamin kudi a dalilin kare jami’an gwamnati marasa gaskiya a kotu, ko ta kare ‘yan siyasa a shari’ar zaben gwamnoni da shugaban kasa.”

“Haka zalika Alkalai da-dama sun yi kaurin-suna wajen cin haram ta hanyar karbar kudi domin su saida shari’a, musamman a shari’ar sauraron korafin zabe.”

“A baya ana zaben tsofaffin Alkalan da suka kusa yin ritaya a matsayin wadanda za su saurari karar zabe, su kuma sai su saida shari’ar ga wanda ya fi kudi.” “Sai su samu kudi, su yi maza su yi ritaya domin su kubuta daga hukuncin majalisar Shari’a.”

Labarai Makamanta