An tsige Manajan Darakta na Hukumar rarraba tallafi a fannin Aikin Gona na kasa (NIRSAL) daga aikinsa. Kamar yadda Jaridar Daily Trust ta ruwaito
Majiyar Dimokuradiyya ta nakalto cewa korar Aliyu Abdulhameed, ba zai rasa nasaba da zarge-zargen cin hanci da rashawa da yawa ba.
A watan Janairun bana ne Daily Trust ta gudanar da bincike kan yadda NIRSAL ke bayar da lamunin rancen biliyoyin Naira na wasu kamfanoni masu zuba jari don noma hekta 20,000 na alkama na noman rani a Kano da kuma Jigawa bisa zargin karkatar da kudaden kamfanonin tare da hadin bakin jami’an NIRSAL.
Abdulhameed ya musanta zargin yana mai cewa wasu mutane marasa kirki ne suka shirya domin bata masa suna da Hukumar.
Sai dai bayan rahoton, jami’an hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta kasa EFFC sun gayyace shi da sauran jami’an NIRSAL domin yi musu tambayoyi kan rawar da suka taka a badakalar aikin alkama.
Baya ga EFCC, ICPC da ‘yan sanda suma sun kaddamar da bincike kan lamarin.
Wasu majiyoyi na cikin gida da suka tabbatar da faruwar lamarin sun ce biyo qbayar, an kori MD din ne da yammacin ranar Alhamis din da ta gabata, aka kuma fitar da shi daga harabar jim kadan bayan ya
Ko da yake har yanzu ba a mika shi a hukumance ba, wata majiya da ba ta so a ambaci sunanta ta ce Hukumar NIRSAL ta bukaci a ba da sunan mukaddashin MD.
Dukkansu MD, Abdulhameed da mai magana da yawun NIRSAL, Anne Ihugba, ba su amsa kira da saƙonnin kartakkwana da aka aika musu ba don amsa wannan lamari ba.
You must log in to post a comment.