Akwai Yiwuwar Gwamnoni Su Yi Sulhu Da ‘Yan Bindiga

Manyan alamu sun bayyana cewa Kungiyar gwamnonin Najeriya na wani shiri domin yin zaman sulhu da miyagun ‘yan bindiga dake addabar kasar musamman yankin Arewacin Kasar da nufin kawo zaman lafiya dawamamme a faɗin Najeriya.

Shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya Dr. Kayode Fayemi ya nuna yiwuwar yin hakan a ranar Talata, bayan ya kai wa gwamnan Jihar Neja, Abubakar Sani Bello ziyarar jaje na garkuwa da ɗaliban Makarantar Kagara da ‘yan Bindiga suka yi.

Gwamna Kayode Fayemi ya ziyarci abokin aikin na sa ne tare da wasu takwarorinsa a garin Minna. Hakan na zuwa bayan garkuwa da mutanen da aka yi a jihar.

“Duk mun san irin ciwon da ka ke ji a zuciya. Mun kuma san tsoro da dar-dar din da mutanen jihar Neja su ka shiga.”

“Wannan ba bakon abu ba ne. Abin da ya faru ya taba faru wa da wasu. Ka na cikin tawagar da ta kai ziyarar jaje Jihar Borno, Katsina Ogun da Oyo.”

Gwamna Fayemi ya ƙara da cewa bai so a rika yawan koka wa, wannan ba shi ne abin da ya kamata ba. “Mutanenmu na neman yadda za a bi a kawo karshen wannan tashin hankali ne kawai.”

“Dole kuma mu duba sauran bangarori daban da aikin da jami’an tsaro su ke yi, idan hakan ya na nufin ayi sulhu ne to ba makawa za mu yi shi.

Shugaban Gwamnonin ya tabbatar da cewa za su yi duk abin da ya kamata domin ganin wannan rikici ya zama tarihi. “Sai mun duba abubuwan da su ka fara sababba wannan rikicin domin gano bakin zaren.

Da yake maida jawabi, gwamnan jihar Neja Abubakar Sani Bello ya ce ya goyi bayan kiran Ƙungiyar Gwamnonin na cewa ayi sulhu, ya ce amma idan har za ayi hakan, a zauna a sasanta ne da tubabbun ‘yan bindigan.

Tawagar Ƙungiyar Gwamnonin da suka ziyarci Jihar sun haɗa Gwamnan Simon Lalong na Jihar Filato, Abdulrahman Abdulrazaq na Kwara sai Abdullahi Sule na Jihar Nasarawa da gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sokoto.

A baya dai kun ji yadda Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya bayyana cewa bai gamsu da matsayar Ahmad Gumi, na cewa gwamnatin tarayya ta zauna teburin sasanci da miyagu ba.

Gwamnan na Jihar Kaduna, ya ce ba’a sulhu da ‘yan ta’adda kuma bai yarda a yi musu afuwa ba. “Ban yarda da wannan ba, miyagun ‘yan bindiga ne, mafi yawancinsu a jeji su ke, mu gano su, mu je mu yi maganinsu.”

Labarai Makamanta