Akwai Tufka Da Warwara A Kundin Tsarin Mulkin Najeriya – Shugaban Majalisa

Shugaban majalisar wakilan Najeriya Femi Gbajabiamila ya ce kundin tsarin mulkin kasarnan na shekarar 1999 ya gaza magance wasu manyan matsaloli da ke addabar kasar, abin da ya sa kenan ‘yan majalisa suka yanke shawarar sauya shi domin dawo dashi bisa ga tsari.

Gbajabiamila ya fadi hakan ne a wajen taron jin ra’ayoyin jama’a kan sauya kundin tsarin mulkin a Legas a ranar Talata, kamar yadda wata sanarwa da mai bai wa majalisar wakilan shawara kan yada labarai ta fitar.

Shugaban majalisar ya ce kundin tsarin mulki ba wai tushen kasa ba ne kawai, kamata ya yi ya zayyana ka’idojin zaman kasa da kuma burikanta na akida da gaskiya, amma “namu kundin tsarin mulkin na cike da nakasu,” a cewar Gbajabiamila.

Ya ce dalilan da suka janyo hakan kuwa har da yadda aka yi gaggawar samar da kundin tsarin mulkin na 1999 don ganin an mayar wa farar hula mulki bayan shafe shekaru masu yawa karkashin mulkin soja.

Sai dai ya ce a wannan karon Majalisar Dokokin za ta iya yin nasarar cimma burin sauya kundin ne kawai idan har ‘yan kasa suka mara wa kokarinta baya tare da ba da gudunmuwarsu.

Labarai Makamanta