Akwai Siyasa Cikin Tabarbarewar Tsaro – Babangida Aliyu

Labarin dake shigo mana daga Minna Babban birnin Jihar Neja na bayyana cewar Tsohon gwamnan jihar Babangida Aliyu, ya ce wasu yan arewa ne suka sa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya kasa murkushe Boko Haram a lokacin Mulkinsa.

Da yake magana a yayin wata hira da jaridar Punch, tsohon gwamnan ya ce abin takaici ne yadda aka bar rashin tsaro ya ta’azzara a Najeriya musamman yankin Arewacin Kasar.

“Lokacin da Boko Haram ya fara sannan gwamnatin Umaru Musa Yar’Adua da Goodluck ta fara yin wani abu a kai, sai lamarin ya fada karkashin Jonathan don ya ci gaba. Yan arewa da dama suka yiwa matsayin Jonathan wani irin fahimta saboda dalilai na siyasa, suna ta korafe-korafe da ya hana aiwatar da manufofin da suka dace wanda da sun kawar da Boko Haram kuma gashi har yanzu muna fama da su”.

“Fashin daji wanda da dama daga cikinmu suka zata ba zai taba faruwa ba, har yanzu ban ji daga kowa ba game da jawabin da aka alakanta da Kawu Baraje, tsohon shugabanmu na PDP na kasa a jihar Kwara, lokacin da ya bayyana cewa sun kawo yan fashin daji ko Fulani daga sauran wurare. Ina ganin bisa tunanin cewa tsohon shugaban kasa Jonathan ba zai mika mulki ba koda sun yi nasara, amma sai ya mika.

“Ya taya su murna tunma kafin a kammala kirga kuri’u wanda ya kawar da duk manufar kawo wadannan mutane kuma da zan yi tunanin cewa idan wannan gaskiya ne, to wadanda suka kawo su za su basu toshiya domin su koma inda suka fito.”

“Idan da gwamnoni sun yi kokari daga 2015 zuwa yanzu, da mun kawar da fashi da makami. “A yau abun takaici ne cewa sai mutum ya yi ta addu’a idan ya bar Abuja zuwa Kaduna ko Kaduna zuwa Abuja ko kuma musamman a jihohin arewa.

“Yanzu hatta da rana, ba za ka iya tuki hankali kwance ba. Don haka, na yarda cewa matakin farko na yakar rashin tsaro sune gwamnoni. Watakila kun ji ni a Kano lokacin da nake cewa shin mutum daya zai iya fin 19 saboda a lokaci daya, koda dai yanayin sun banbata, muna da mutum daya kan jihohi 19 sannan a yanzu muna da gwamnoni 19 amma duk da haka muna da matsaloli fiye da yadda muke da su a baya.”

Labarai Makamanta