Akwai Siyasa A Matsalar Tsaro Da Najeriya Ke Ciki – Buratai

Tsohon hafsan Sojin Najeriya, Laftanan Janar Tukur Yusuf Buratai (mai murabus), ya bayyana cewar da akwai manyan kalubale da sha’anin tsaro ke fuskanta a kasar nan, wanda suka haɗa da Siyasa, bangaranci da sauransu, wanda hakan ke haifar da Cikas a kokarin da Gwamnati ke yi na yaki da ta’addanci a ƙasar.

Buratai ya yi wannan furuci ne a lokacin da ya bayyana gaban majalisar dokokin tarayya domin tantance shi a matsayin Jakada a ranar Alhamis, inda ya ce da yiwuwar wannan rikicin na Boko Haram ya cigaba har tsawon shekaru ashirin masu zuwa.

Ya ce da dadewa, yan ta’addan sun canza akidun mutane, kuma hakan zai sa kawo karshen yakin ya zama abu mai matukar wuya.

Tsohon Sojan ya ce duk da cewa Sojojin Najeriya na samun hadin kai daga kasashe makwabta irinsu Kamaru, Chadi da Nijar, kuma ana samun nasara, amma karfin bindiga kadai ba zai kawo karshen yakin ba.

Buratai ya ce akwai matsalolin siyasa da tattalin arziki da ya kamata a magance tukunna, saboda yawancin garuruwan Arewacin Najeriya na da karancin abubuwan more rayuwa.

“Sojojinmu na hada kai da Sojin Chadi da Kamaru. Mun samu nasarori. Amma yan ta’addan sun ratsa zukatan al’umma,” yace. “Jihata Borno ce hedkwatar inda akayi masifar ratsa zukatan mutane sosai.

Ba abu ne wanda za’a iya cirewa a dare daya bane.” “Sojoji kadai ba zasu iya magance matsalan ba. Akwai matsalolin tattalin arziki da ya kamata a magance. Ya kamata akwai kayan more rayuwa, amma babu.

“Zan iya fada muku kananan hukumomi biyar a jihar Borno da babu hanyoyi masu kyau. Hakazalika Zamfara, Katsina da Sokoto. Akwai wurare da dama a Arewa da babu alaman gwamnati saboda babu hanyoyi da kayan jin dadi,””Za mu kwashe shekaru 20 bamu gama yakin ba.”

Labarai Makamanta