Akwai Salihan Bayi Cikin ‘Yan Bindiga – Matawalle

Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawallen Maradun ya ce ba duka tsagerun ‘yan bindiga bane mutanen banza, akwai bayin Allan mutanen ƙwarai a cikin su, wasu dole ce ta wajabta musu daukar bindiga.

Gwamnan ya bayyana hakan ne ga manema labarai bayan ganawa da shugaba Buhari a fadar shugaban kasa ranar Alhamis, 18 ga Febrairu, 2021, inda ya ƙara da cewa yawancin ‘yan bindigan sun shiga harkar ne saboda irin rashin adalcin da al’ummar gari ke nuna musu.

“Ba dukkansu bane mutanen banza. Idan ka bincike abinda ke faruwa, da kuma abinda ya sa suka dauki doka a hannunsu, wasu daga cikinsu sun fuskanci zalunci ne daga wajen yan banga,” inji Matawalle.

“Su (Yan bangan) kan kai musu hari a rugarsu, su lalata musu dukiya kuma su kwashe musu dabbobi. Babu wanda zasu kai wa kara, shi yasa wani lokaci suke daukan fansa.”

“Wasunsu na zama a kauyuka kusa da gari. Duk lokacin da Sojoji suka kai hari, su kan lalata musu dukiya da dabbobi. Suna jin haushin wadannan abubuwa. Idan ka tattauna da su, za ka fahimci wadannan abubuwa.”

A bangare guda, Auwal Daudawa, wanda ya jagoranci sace daliban Makarantar Sakandaren Kimiyya ta Gwamnati dake Kankara, Jihar Katsina, ya ce ya jagoranci wannan samamen ne saboda Gwamna Bello Masari ya ci amanar dakarunsa.

A wata tattaunawa ta musamman da ya yi da jaridar Daily Trust, Daudawa ya ce yana so ya tabbatar wa da gwamnati cewa yana da karfin da zai kai irin wannan harin a koda yaushe lokacin da ya ga dama.

Labarai Makamanta