Akwai Muggan Makamai Sama Da Miliyan 6 Dake Karakaina A Najeriya – Abubakar

Tsohon shugaban ƙasa na mulkin Soja, Janar Abdulsalami Alhaji Abubakar mai ritaya, ya yi tsokaci gami da gargaɗin ‘yan Najeriya kan yawaitar Miliyoyin muggan makamai dake karakaina a faɗin kasar nan.

Janar Abdulsalami Abubakar ya ce da akwai muggan makamai dake shawagi a cikin Najeriya sama da miliyan Shida ba bisa ƙa’ida ba, kuma sun wadatu a hannun ‘yan ta’adda.

Abdussalami Abubakar, wanda shine shugaban kwamitin zaman lafiya a Najeriya (NPC) ya yi wannan gargaɗi ne a wani taro da suka yi da masu ruwa da tsaki a Abuja ranar Laraba.

Abdussalami ya ce, yawaitar makaman a ƙasa shine yake jawo ƙaruwar matsalolin tsaro da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da dubu 80,000 galibin su mutanen Arewa.

Ya ce ƙalubalen da ƙasar nan ke fuskanta bawai rashin tsaro ne kaɗai ba, akwai wasu matsalolin na rayuwa masu nasaba da talauci da kuma jahilci dake cigaba da mayar da hannun agogo baya.

Tsohon shugaban kasar ya bayyana ƙalubalen da Najeriya ke fuskanta kamar; Rikicin Boko Haram, fashi da makami, satar mutane domin neman kuɗin fansa, ƙaruwar talauci da tsadar rayuwa, kira ga rarraba ƙasa da wasu ke yi, ta ko’ina abin babu sauki.

Ya ƙara da cewa akwai ƙalubalen yunwa da rashin tsaro ke jawo wa, wanda manoma ke fuskanta kuma suke cigaba da fuskanta, da dai sauran su. Ya ce wata matsalar kuma itace yawaitar muggan makamai dake yawo, ba wai a wasu yankuna kaɗai ba, a faɗin ƙasar baki ɗaya.

Ya kara da cewa a halin yanzun ana ƙiyasin akwai sama da makamai miliyan Shida dake yawo a faɗin ƙasar nan. Wanda wannan shine yake ƙara yawaitar matsalolin tsaro, wanda ya jawo mutuwar mutane sama da 80,000 da kuma fitar da mutane kusan miliyan uku daga mahallinsu.

Tsohon shugaban mulkin sojan ya ce jami’an tsaron mu zasu yi matuƙar ƙoƙari wajen shawo kan matsalar idan aka samar musu da makaman da yakamata da kuɗaɗe yadda yakamata.

Labarai Makamanta