Akwai Gyara A Harkar ‘Yan Kannywood – Adam Zango

Shahararren dan wasan Hausa fim na masana’atar Kannywood Adam Zango ya bayyana cewar da akwai gyara a yadda harkar ta su ke tafiya a halin yanzu da ya kamata a ɗauki matakin gyara.

Adam Zango na bayani ne a yayin mayar da martani dangane da sukar da malaman addini da sauran jama’a ke yi musu na bata tarbiyya maimakon gyaranta.

Jarumin ya ce tabbas idan har ɓera da sata babu shakka daddawa ma ta wari, yadda harkar ‘yan fim ke tafiya a yanzu abin takaici ne, an kai ga matsayin cin mutunci da wulakanta juna a tsakaninsu musanman akan abin da ya shafi harkar siyasa.

*Akwai waɗanda ni ne silar su zuwa Kannywood amma a yanzu babu wanda suke ci wa mutunci kamar ni, Lallai wannan abin takaici ne da ya kamata mu gyara gaba daya”

“Da wuya ka ga ‘yan Fim a wajen taron da ya shafi Addini saidai a wajen tarukan sharholiya”

Labarai Makamanta