Akwai Dalilin Da Yasa Ba Za Mu Murkushe ‘Yan Bindiga Ba – Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari cikin tsananin fushi ya gargadi ‘yan bindiga da ke adabar al’umma a sassan kasar musanman Arewacin Najeriya da cewa gwamnatinsa za ta iya yin maganin su, cikin ƙanƙanin lokaci ba domin wani dalili ba.

A cikin sanarwar da ya fitar, mai magana da yawun shugaban kasa Garba Shehu ya ce shugaban kasar ya nuna damuwarsa kan karuwar ayyukan bata gari a ƙasar inda ya ce ba domin ana iya amfani da wadanda aka sace a matsayin garkuwa ba wanda zai haifar da salwatar rayyuka, da tuni jami’an tsaro sun gama da su.

Shugaban kasar ya bayyana satar ɗaruruwan ɗaliban na GGSS Jangebe a jihar Zamfara da ɗaliban Kagara ta Jihar Neja a matsayin rashin tausayi da tsagwaron rashin imani kuma ba za a amince da shi ba.

“Wannan gwamnatin ba za ta lamunci harin da ‘yan bindiga ke kai wa yaran makaranta ba da nufin samun kudin fansa. “Su daina bari magagi na dibansu suna ganin kamar sun fi karfin gwamnati ne. Kada su dauki kame kan da muke yi domin kare rayuwar wadanda ba su-ji-ba -ba-su-gani ba a matsayin tsoro, “

Shugaban kasar ya yi kira ga gwamnatocin jihohi su yi bita kan tsarinsu na sakawa ‘yan bindiga da kudade da motoci, inda ya yi gargadin hakan na iya karfafawa wasu cigaba da kai hare-haren.

Ya shawarci jihohi da kananan hukumomi su dauki matakan samar da tsaro a makaratu da garuruwan da ke kusa da makarantun.

Labarai Makamanta