Aisha Buhari Ta Zama Shugabar Matan Shugabannin Afirka

Kungiyar matan shugabannin kasashen Afrika ta Kudu (AFLPM) ta zabi Aisha, uwargidan shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin shugabar ta a ranar Litinin a Abuja, a wani babban taronta da ta gudanar karo na 9 a Nigeria.

Zaben nata ya gudana ne a yayin taron hukumar zartarwa karo na 5 na kungiyar.

A jawabinta na karba, Aisha ta yi alkawarin ba da lokacinta da karfinta wajen inganta zaman lafiya da magance rikice-rikice a nahiyar Afirka.

“Tare da kaskantar da kai, na amince da zabena a matsayin shugaban tawagar mata masu zaman lafiya ta kasashen Afirka a taro na 9 na babban taron kungiyar Matan shugabannin kasashen Afrika.

“Ina so na gode muku da gaske saboda goyon baya da fahimta tare da ba ni amana da wannan babban aiki.

“Na yi alƙawarin aiwatar da alhakina tare da jajircewa kuma bisa ka’idojin da aka gindaya. Kamar yadda kuka san aikin da ke gabanmu yana da girma, don haka ana buƙatar gudunmawar ku.

“Ina tabbatar muku cewa, zan sauke nauyin da ke kaina bisa gaskiya, sadaukarwa da kuma hada kai,” kamar yadda ta shaida wa ‘yan majalisar.

Jaridar Dimukuradiyya ta ruwaito cewa an kafa kungiyar ta AFLPM a shekarar 1997 a matsayin kungiyar matan shugabannin kasashen Afirka.

An kafa ta ne domin ta taka rawa ga kungiyar Tarayyar Afirka, kungiyoyin shiyye-shiyya da gwamnatocin kasashe wajen samar da zaman lafiya da rage rikice-rikice a nahiyar ta Afrika.

Labarai Makamanta