Aisha Buhari Ta Yi Kiran Mata Su Rungumi Sana’ar Kwallon Kafa

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari ta yi kira ga mata su rungumi kwallon kafa a matsayin sana’a.

Ta sanar da hakan ne a lokacin da take tarbar shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya, FIFA, Gianni Infatino a fadar gwamnati da ke Abuja.

Wata sanarwar da mataimakinta kan yada labarai, Aliyu Abdullahi ya fitar ta ambato uwargidan na cewa ta hanyar kwallon kafa ana iya inganta daidaito da samar da ci gaba.

Sannan ta ce tana hada-kai da NFF wajen inganta wasan kwallon kafa tsakanin mata a Najeriya da duniya baki ɗaya ta hanyar kofin da ta sa na ‘Aisha Buhari’.

Ta bukaci hukumomin FIFA da CAF da NFF su sake nuna goyon-baya da kwarin-gwiwa ga mata masu kwallon kafa a matakin gida da wajen kasar.

Sannan ta yabi shugaban FIFA bisa goyon-bayan da yake nunawa kwallon kafar mata da gudunmawa da yake basu.

Ana sa ɓangaren shugaban FIFA ya yabawa Aisha Buhari bisa namijin kokarinta wajen raya tamaulan mata da karfafa musu gwiwar kai wa ga wani mataki na rayuwa.

Mista Infantino ya zo Najeriya ne da rakiyar shugaban hukumar CAF, Patrice Motsepe da na NFF Amaju Pinnick da sauran wasu jami’an hukumomin.

Labarai Makamanta

Leave a Reply