Aisha Buhari Ta Gwangwaje Matasan Najeriya Da Tallafi

Matan Najeriya da matasa da dama a yanzu haka sun ci gajiyar shirin tallafi da Aisha Buhari ta kirkiro, domin saukaka musu raɗaɗi na wahalar rayuwa.

Uwargidan shugaban kasar a ranar Alhamis, 25 ga Maris, ta raba kayan fara aiki ga wadanda suka ci gajiyar a kokarin ta na ganin sun zama masu cin gashin kansu.

Wannan aikin alkhairin wanda ke zuwa bayan dawowar Aisha daga Dubai a kwanan nan, an fara shi ne kafin barkewar cutar COVID-19.

Da alama Aisha Buhari, ta dawo daga Dubai ne tare da kyawawan abubuwan alheri ga ‘yan ƙasa, musamman ga mata.

A wani taron da aka gudanar a ranar Alhamis, 25 ga watan Maris, uwargidan shugaban kasar ta baiwa mata da matasa tallafi na keken dinki, injin saka, da kuma kayan aikin noma domin kama sana’a.

Ofishin Uwargidan shugaban kasar ne ya kirkiri wannan shirin kuma ya fara ne tun kafin billowar cutar COVID-19.

Uwargidan shugaban kasar ta yi kira da a kara samar da tsare-tsare ga mata da matasa daga gwamnatin tarayya da kungiyoyi masu zaman kansu.

A baya mun ji cewa Uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari, ta dawo gida Najeriya bayan watanni shida a birnin Dubai, kasar haddadiyar daular Larabawa.

Labarai Makamanta