Aikin Soja Ba Sana’ar Neman Kudi Bane – Shugaban Dakarun Soji

Babban Hafsan Sojojin Najeriya, Faruk Yahaya ya bayyana cewa masu hanƙoron shiga aikin soja su saka a ran su cewa za su shiga ne domin kishin ƙasa da sadaukarwa gare ta, amma su daina yi wa aikin soja wani wurin samun aiki.

Ya ce aikin soja aiki ne na kare Najeriya, ba wurin aikin samun kuɗi ba ne.

Laftanar Janar Yahaya ya yi wannan nunin a lokacin da ake wa masu neman shiga aikin kuratan sojoji gwanin juriyar gudun kilomita 10.

An ƙaddamar da yi masu gwajin ne a Cibiyar Gwajin Horon Sabbin Suratan Sojoji da ke Dajin Falgore, Jihar Kano.

Wannan bayani na Laftanar Janar Yahaya na ƙunshe a cikin wata sanarwar da Kakakin Hulɗa da Jama’a na Sojojin Najeriya, Onyema Nwachuku ya fitar a ranar Asabar, a Abuja.

Ya ce shiga aikin soja ba kamar samun aiki ba ne a wasu fannoni na rayuwa, shi aikin soja aiki ne na sadaukarwa ɗungurugum wajen kare Najeriya.

Ya ce waɗanda ake buƙata su shiga aikin soja, su kasance lafiyar su garau, jikin su gagau, ganin su rangaɗau, ƙwaƙwalwar saɗai ta ke babu wani dattin taɓin hankali, wauta, buguwa, gargajiganci ko kuma alamomin ɗabi’un shagirigirbau a jikin mutum.

“Aikin soja ba aiki ne da kowane ke iya shiga ba. Ba wurin neman kuɗi ba ne. Aiki ne na sadaukar da rayuwa domin a kare ƙasa kawai.”

Daga nan Yahaya ya shawarci masu neman shiga aikin soja ɗin su ɗauki wannan tantancewa da ake yi masu da muhimmancin gaske.

Labarai Makamanta