Ahmed Musa Zai Koma Wasa Kasar Turkiyya

Mai jan ragamar babbar kungiyar kwallon kafa ta Najeriya watau Super Eagles, Ahmed Musa zai bar kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars izuwa kasar Turkiyya a karshen sati mai zuwa.

A wani rahoton, wata kungiyar kwallon kafa a kasar Turkiyya ta baiwa Dan wasan kwantiragin shekara daya a kan kudi biliyan 1.05.

Jaridar Complete Sport cewa tayi, mai kungiyar kwallon kafan yace badan cutar Covid-19 ba da zai kara masa sama da haka, duba da yadda cutar Covid-19 ta karya tattalin arziqin kungiyoyin kwallon kafa ta nahiyar turai baki daya.

Yace yanzu dai muna burin ganin Dan wasa Ahmed Musa a cikin jerin Yan wasan mu a kakar wasanni mai zuwa.

Ahmed Musa ya amince da bugawa kungiyar kwallon wasa.

Dan wasan mai shekaru ashirin da takwas zai je kasar Turkiya karshen sati mai zuwa don rattaba hannu kan Yarjejeniyar.

Idan baku manta ba a 13 na watan Aprilu ne Dan wasan ya koma Kano Pillars don karkare kakar wasanni ta 2020/2021.

Daman can dai yayima kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars alkawrin barin kungiyar da zaran ya samu wani kwantiragin.

Labarai Makamanta