Ahmed Musa Zai Koma Kano Pillars

Dan wasan mai shekara 28, wanda ba ya buga wa kowacce kungiya tamaula tun da ya bar Al Nassr ta Saudiyya a watan Oktoba, ya samu tayin tafiya Ingila da Rasha da kuma Turkiyya.

Sai dai a yayin da yake nazari kan matakin da zai dauka na tafiya wata kasar Turai a bazara, dan wasan ya karbi goron gayyata daga gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje da Shehu Dikko, shugaban League Management Company (LMC) domin ya murza leda a Pillars.

Tsohon ɗan wasan na Leicester City ya shaida wa BBC Sport Africa. cewa: “Bayan na yi magana da gwamna da shugaban LMC ina duba yiwuwar murza tamaula a Kano pillars.”      “Zan yi duk abin da zai fito da mutuncin kwallon kafar Najeriya kuma ina kallon Kano Pillars da matukar muhimmanci.

“Ita ce kungiyar da ta taimaka mini na zama shahararren dan wasan kwallon kafa a yau, don haka wannan dangantaka ta wuce ta kwallon kafa danganaka ce mai yauki.”

Wata majiya da ke kusa da kungiyar ta shaida wa BBC Sport Africa ana dab da kammala kulla yarjejeniyar dawo da Musa Kano Pillars.

Musa, wanda ya bude gidajen koyon kwalon kafa da atisaye biyu a arewacin Najeriya, ya ci wa Kano Pillars kwallaye 18 lamarin da ya sa ta yi nasarar lashe kofin lig na Najeriya a kakar wasan 2009/10.

Musa ya buga wa Najeriya kwallo sau his 96 inda a wasansu na baya bayan nan Super Eagles ta doke Lesotho da ci 3-0 a birnin Lagos inda ta samu gurbin zuwa gasar cin Kofin Nahiyar Afirka.

Labarai Makamanta

Leave a Reply