Ahmed Musa Ya Bada Gudummuwar Miliyan Biyu Domin Gina Masallaci

Rahotanni daga birnin Kano na bayyana cewar ɗan Kwallon Nijeriya, Ahmed Musa Ya Bada Tallafin Naira Milyan Biyu Domin Gina wani katafaren Masallaci a birnin Kano.

Za a gina masallacin ne a makarantar sakandire ta sojoji dake Barikin Bukavo a jihar Kano.

A kwanakin baya ne dai Ahmed Musa ya shelanta cewa ya dawo buga wasan ƙwallon kafa a Ƙungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars dake Kano.

Masana dai sun bayyana Ahmed Musa a matsayin ɗaya daga cikin attajiran ‘yan wasan ƙwallon ƙafa a duniya wanda tauraron su ke haskawa.

Labarai Makamanta