Afuwa Ga ‘Yan Bindiga Ne Maganin Matsalar Tsaro – Dr Gumi

Shahararren malamin addinin musulunci a Najeriya, Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi, ya bayyana cewar hanya guda wadda ta ragewa Najeriya na samun zaman lafiya shine Gwamnati ta yi sulhu da ‘yan bindiga sannan ta yafe musu zunubban su domin samun zaman lafiya mai dorewa.

Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya ce idan za a iya yi wa wadanda su ka kifar da gwamnati afuwa, babu laifi don a yafe wa ‘yan bindiga.

Malamin ya na wannan magana ne a ranar Alhamis, 4 ga watan Maris, 2021. Shehin ya maida martani ne ga kungiyar Kiristocin Najeriya watau CAN a garin Kaduna.

Ahmad Gumi ya ce akwai bukatar ayi afuwa saboda a zauna lafiya abin da ya sa muke neman ayi sulhu da ‘yan bindigar ne.

“Har wadanda su ka haddasa yakin basasa, yakin da ya ci miliyoyin mutane, an yafe masu. Ban ga dalilin da ba za mu amince da tuban ‘yan bindiga ba.”

Dr. Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya ce ya kamata gwamnati ta yi lamuni, ta yafe wa miyagun. Babban malamin ya yi karin-haske game da wasu kalamai da aka ji ya yi, yake cewa kungiyar CAN ba ta fahimce shi ba ne, saboda an rikidar da maganarsa.

“Ku na tambaya meyasa mu ke neman ayi masu lamuni? Sun fada mana cewa sun shirya ajiye makamai, amma ba su son a bi su da kara a kotu bayan sun tuba.”

Labarai Makamanta