Afuwa Ga ‘Yan Bindiga Ne Mafita Ga Matsalar Tsaro Da Ake Ciki – Gumi

An bayyana cewar hanya guda ɗaya tilo da ta saura a Najeriya na magance matsalar tsaro dake addabar kasar musanman yankin Arewacin Najeriya shine Gwamnati ta yi afuwa ga ‘yan Bindiga a karbesu matsayin Mutane.

Mashahurin Malamin addinin Islama kuma mai shiga tsakani a yaƙin da ake yi na kawo karshen matsalar ‘yan ta’adda a Najeriya, Sheikh Dr. Ahmad Abubakar Mahmoud Gumi ya bayyana hakan a ganawar shi da manema labarai a Kaduna.

Sannan ya bukaci gwamnatin tarayya da ta yi amfani da shawarwarinsa tare da yin afuwa ga’ yan ta’addan da za su ajiye makamansu domin kawo karshen matsalar gaba ɗaya.

Dr Ahmad Gumi ya bayyana hakan ne a lokacin da yake mayar da martani game da kisan wasu dalibai uku na jami’ar Greenfield Kaduna, da wasu yan bindiga suka sace su daga makarantarsu.

Malamin ya ce ba shi da katabus game da lamarin jihar Kaduna saboda gwamnatin jihar ba ta nuna kowane irin shiri na tattaunawa da ‘yan bindigar ba.

Sannannen Malamin ya ƙara da cewar hanya daya tilo da zai sa baki kamar yadda ya yi a jihohin Neja da Katsina ita ce El-Rufai ya sake shawara game da tattaunawa da ‘yan Bindigar.

“Lamarin ya fara munana kuma ina bukatar goyon bayan gwamnati kafin na iya yin komai, kuma ina ganin akwai babban rashin fahimta da karancin karanta halin da ake ciki a kasa. Don haka, bani da katabus; Ban san ainihin abin da zan iya yi ba a yanzu.”

Gumi ya bayyana kisan daliban Greenfield a matsayin mai halakarwa, abin takaici kuma wanda bai dace ba, yana zargin cewa yaƙin ƙabilanci na gudana a kasar.

“Maganar gaskiya, abin takaici ne matuka. Akwai yaƙin ƙabilanci dake gudana, kuma na sha fadarsa. Yaƙi ne amma idan ba ma son yarda da cewa yaƙi ne, za mu ci gaba da shan wahala.”

Labarai Makamanta