Addu’a Shugabanni Ke Buƙata Wajen Talakawa – Lawan

Shugaban majalisar dattijai, Dakta Ahmad Lawan ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su ci gaba da yi wa shugabannin gwamnati addu’a a kokarinsu na tunkarar matsaloli daban-daban da kasar ke fuskanta.

Lawan ya yi wannan kira ne a jiya Asabar a wajen kaddamar da asusun tallafi na Masallacin Masarautar Potiskum a garin Potiskum dake Jihar Yobe.

Shugaban majalisar dattijan da ya sanar da bayar da gudummawar Naira miliyan 20 don tallafawa aikin ya ce: “A kowane lokaci shugabanni na bukatar addu’o’i musamman daga mabiya.

“Shugabanninmu, musamman Shugaban kasarmu, Muhammadu Buhari, da fatan Allah Ya ba shi lafiya, Allah Ya ba shi jagorancin kasar nan ne ta dalilinku.

“Yana kokari iyakar kokarinsa a gare ku kuma mu ma da muke daga bangaren shugabancinsa, muna kokari iyakar kokarinmu don ganin cewa abubuwa sun daidaita a Nijeriya.

Labarai Makamanta