Addu’a Ce Mafita Ga Halin Da Najeriya Ke Ciki

Daga muhammad Sani Yusuf Nassarawa

A daidai lokacin da ake kara shiga cikin dimuwa da rashin Tabbas na samun Tsaro a kasarnan Musamman a yankin Arewa wanda Matsalar Tsaron tafi shafarsu kama daga kona musu Muhalli tare da kayan abincin da suka tanada da kuma hana yankin Arewa Gudanar da sana arsu ta gado wato Noma da kiwo tunidai wannan ya zama Tarihi a yankin

Shin Ko yaushe Talakan Kasarnan zai fahinci ana yin Dumukradiyya wacce ake cewa itace yancin Talakan?

Maganar Gaskiya dai Itace Tuni talakawan Kasarna suka hakura da batun Samar da Tsaro wanda shine Babban Aikin da yake Gaban Kowacce Gwamnati

To Saidai kash a gefe Guda Jama a da dama na ganin Wannan Gwamnatin ta gaza akan Alkawarin da ta Dauka tun Farkon Kama Mulkinsu

Duk da cewa Gwamnatin da ta Gabata ta Fuskanci Irin wannan Kalubale na tsaro wanda hakan yayi sanadiyyar Jama ar kasar suka gudanar da Bore tare da zanga zanga wanda ya haifar da Kin jinin Gwamnatin har yakai ga sauya ta da wannan Gwamnatin da take kai

Bisa ga Dukkan alamu Itama wannan Gwamnatin an dauko Hanya na aiwatar da Bore sakamakon Halin da Kasar take ciki

Wannan Mataki da yan kasa suka fara Dauka na Bore ya farane daga yin boren ta hanyar kin jinin abinda ke faruwa a wuren Hira a Majalisu da shafin sadarwa na yanar Gizo da sauransu

Akwai wata Baiwar Allah daga jihar Kano da ta Dauki aniyar gudanar da zanga zanga amma wani abin Daure Kai sai wani labari muka gani yana yawo cewa Hukumar DSS ta gayyace ta bayan ta Dawo sai kwatsam tace ta janye daga gudanar da wannan zanga zanga

Wannan labari ya jefawa Mutane Shakku a zuciya na neman sanin Dalilin janyewar wannan Kuduri nata

Yanzundai Tuni Shafukan sada Zumunta Suka fara sanya irin Abubuwan da suka faru Kafin Wannan Gwamnati ta Hau Mulki Musamman na Alkawuran da suka dauka na samar da tsaro Tattalin Arziki Samar da aikin yi ga Matasa da sauran Alkawuran da suka Gabata a Shekara ta 2015

Abin Tambaya anan Shine Ko Wannan Gwamnatin zata iya Cika Alkawarin da ta Dauka kafin Wa a dinta ya kare?
Wannan Kuma Lokaci Kadai ka iya Tabbatar da hakan

Labarai Makamanta