Adamawa: ‘Yan Sanda Sun Ceto Mutanen Da Aka Yi Garkuwa Da Su

Rundunan ‘yan sandan jihar Adamawa tayi nasaran ceto wasu mutane shida wadanda akayi garkuwa da su a tsaunin dutsen dake Garin Mulleng dake cikin karamar hukumar Song a jihar Adamawa.

Kakakin rundunan ‘yan sandan jihar Adamawa DSP Suleiman Yahaya Ngoroje ne ya bayyana haka a wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a Yola.

DSP Suleiman Yahaya Nguroje yace an samu nasaran ceto wadanda akayi garkuwa da su din ne tare da hadin gwiwar Jami an tsaron farin kaya wato DSS da kuma mafarauta biyo bayan musayar wuta da akayi da ‘yan bindigan wanda hakan yasa aka fatattaki ‘yan bindagan daga maboyarsu. Baya ga mutanen shida da aka ceto an kuma an samu bindiga kiran Ak 47 da Harsasai.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Adamawa CP Ahmed Muhammed Barde ya yaba wa rundunar dama takwarorinsu na tsaro bisa wannan namijin kokari da suka yi na ceto mutanen da akayi garkuwa dasu.

CP Muhammed Barde ya tabbatarwa gwamnatin jihar Adamawa dama al’ummar jihar baki daya cewa rundunar a shirye take da kare rayuka dama dukiyoyin al’ummar jihar baki daya.

Don haka nema Kwamishinan ya kirayi al’ummar jihar da su kasance masu bai wa Jami’an tsaro hadin kai da goyon baya domin ganin Rundunar ta cimma burinta na kawo karshen dukkanin kalubalen tsaro dake ciwa gwamnatin jihar tuwo a kwarya.

Labarai Makamanta