Adamawa: ‘Yan Sanda Sun Bindige Masu Garkuwa Shidda

Rundunan ‘yan sandan jihar Adamawa tayi nasaranr hallaka mutane shida tare da kama wasu shida da ceto wani yaro dan shekaru bakwai da haihuwa daga hannun masu garkuwa da mutane domin neman kudin fansa.

Mutanen dai sun gamu da ajalinsune biyo bayan diran mikiya da jami’an ‘yan sandan suka yi a maɓoyar masu garkuwa da mutanen wanda hakan ya haifar da musayar wuta a tsakaninsu, inda ‘yan sandan sukayi galaba akansu.

Da yake yiwa manema labarai ƙarin haske dangane da lamarin, Kwamishinan ‘yan sandan jihar Adamawa Sikiru Kayode Akande yace sun samu nasarar ne tare da hadin kan al’umma jihar Adamawa harma da mafarauta da dai sauransu.

Da wannan yake kira ga al’ummar jihar da su cigaba da ba rundunan hadin kai da goyon baya domin ganin rundunan ta cimma burinta na dakile ayyukan ta’addanci a faɗin jihar baki daya.

Labarai Makamanta