A yanzu haka dai hukumar gudanarwan Kwalejin horar da Malamai ta tarayya wato F C E Yola, ta bada umurnin rufe kwalejin zuwa lokaci biyo bayan tarzoma da ɗaliban kwalejin sukayi a ranar Talata.
Hukumar ta dauki matakin rufe kwalejin ne a lokacin da rijistaran Kwalejin Gidado Ahmed ya zanta da manema labarai dangane da lamarin a Yola.
Gidado yace daukan matakin haka ya zama wajibi domin ganin an shawo kan rikicin, inda yace ɗaliban sun barnata abubuwa da dama wanda zai yi sanadiyar asaran dukiyoyi masu yawa.
Daliban dai sun dauki matakin tayar da tarzoman ne bisa abinda sukace an kara musu kudin makaranta da rashin ruwan sha a kwalejin da sauransu.
Yanzu haka dai an umurci dukkanin ɗaliban sun fice daga kwalejin ya zuwa lokacin hada wannan rahoto komai ya koma dai dai biyo bayan tura Jami an ‘yan sanda domin yafawa rikicin ruwa.
You must log in to post a comment.