Adamawa: Shugaban ‘Yan Kasuwar Arewa Ya Janjanta Wa ‘Yan Kasuwar Kurmi

Biyo bayan gobara da ta lashe shaguna dama dukiyoyi masu yawa a kasuwar kurmi dake jihar Kano hakan yasa al’umma ke ta bayyana alhininsu dangane da aukuwar lamarin.

Da yake nuna alhininsa dangane da tashin gobarar shugaban kungiyar yan kasuwar Arewacin Najeriya Alhaji Muhammed Ibrahim 86 ya jajintawa gwamnatin jihar Kano dama wadanda lamarin ya shafa tare dayin addu’ar Allah Madaukakin sarki ya kare ya kuma mayar masu da mafi alheri.

Alhaji Ibrahim 86 ya kuma kirayi gwamnatin tarayya dana jiha dasu kaiwa wadanda lamarin ya shafa dauki domin kaucewa shiga wahala sakamokon tashin gobarar.

Ya kuma shawarci ‘yan kasuwa da su kasance masu kashe dukkanin kayayyakin da ke amfani da wutan lantarki wanda acewarsa hakan zai taimaka wajen dakile tashin gobara a kasuwanni.

Labarai Makamanta