Adamawa: Rundunar ‘Yan Sanda Ta Yi Babban Kamu

Rundunan yan sandan jihar Adamawa tayi nasarar cafke mutane goma sha uku wadanda ake zargi da aikata lafika daban daban a fadin jihar ta Adamawa.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Sikiru Kayode Akande ne ya bayyana haka a lokacin da yake gabatarwa manema labari wadanda ake zargin a shelkwatan Rundunar dake Yola.

Kwamisihinan ‘yan sandan ya kara da cewar Rundunar ta kuma kama daya daga cikin wadanda ake nema ruwa a jallo wadanda suka gudu daga gidan yari kuje a Abuja bayan hari da aka kai a gidan yarin. Wanda aka kamandai mai suna Abubakar Muhammed dan shekaru ashirin da uku da haihuwa wanda kuma tunin kwamishinan yan sandan ya mikaahi ga kwanturilan gidajen yarin dake jihar Adamawa.

Kwamishinan yan sandan ya jinjinawa Jami’an yan sandan bisa namijin kokarin da sukeyi na zakulo bata gari a cikin al’umma tare da godewa al’umman jihar Adamawa saboda irin goyon baya da suke ba Rundunar don haka nema yana mai tabbatarwa jama ar jihar cewa rundunar a shirye take ta kare rayuka dama dukiyoyin Al’umma baki daya.

Labarai Makamanta