Adamawa: Rundunar ‘Yan Sanda Ta Bukaci Jam’iyyu Su Mika Jadawalin Neman Zabe

Rundunan ‘yan sandan jihar Adamawa ta nemi da jam’iyyun siyasar dake fadin jihar da su mikawa rundunar jadawalin tsarin gangamin neman zabe domin ba rundunan damar dauka dukkanin matakai da suka dace domin dakile duk wata fitnina.

Rundunan ta bayyana haka ne a wata sanarwa da kakakin rundunan yan sandan jihar Adamawa SP Suleiman Yahaya ya fitar wanda aka rabawa manema labarai a Yola.

A cikin sanarwar an jiyo kwamishinan ‘yan sandan jihar Sikiru Kayode Akande na cewa akwai bukatar jam’iyyun su gabatarwa rundunan jadawalin gangamin yaki neman zaben tare da shawartansu da su kasance masu gudanar da ayyukan su bisa tsarin doka.

Ya kuma kirayi Al’umma da suma su kasance masu bada tasu gudumawar wajen samar da tsaro domin samun cigaban zaman lafiya a lokaci dama bayan zabe.

Harwayau kwamishinan ya gudanar da taro da shugabanin hukumomin tsaro dake fadin jihar ta Adamawa dangane da yadda ake kokarin fara gangamin yakin neman zabe.

Kwamishinan ya kuma kirayi Sarakunan gargajiya da su ba rundunan hadin kai da goyon baya domin ganin rundunar ta samu nasarar dakile ayyukan ta’addanci a fadin jihar baki daya.

Labarai Makamanta