Adamawa: Manoma Sun Yi Farin Ciki Da Kaddamar Da Dalar Shinkafa

Manoma a jihar Adamawa na bayyana farin cikinsu dangane da yadda gwamnatin tarayya karkashin Babban Bankin Najeriya wato CBN ta kaddamar da dalan buhunan abinci, biyo bayan gudanar da tsarin nan na Anchor Browas.

Wani shahararren manomi a jihar Adamawa Alhaji Adamu Jingi wanda akafi sani da maihangene ya bayyana haka a zantawarsa da Muryar ‘yanci dangane da Dalan kayayyakin abinci a Najeriya.

Alhaji Adamu yace wannan ya nuna cewa Najeriya zata iya ciyar da kanta harma zata iya fitar da kayayyakin abinci zuwa kasashen waje, a cewarsa dai manoma a Najeriya a shirye suke su rungumi harkokin noma domin ganin an samu damar bunkasa tattalin arzikin kasan nan baki daya.

Saboda haka nema Alhaji Adamu Jingi ke kira ga gwamnatin tarayya da ta kara himma wajen shigo da na’urorin ko injunan aikin noma na zamani, domin rashin kayayyakin noma na zamani ya na ciwa manoma tuwo a kwarya.

Alhaji Adamu yace idan har manoma zasu samu ingantanccen iri, sanadarin feshi, taki, tallafi, da dai sauransu, tofa matsalar noma zai zama tarihi Najeriya.

Harwa yau ya kirayi gwamnatin tarayya dana jihohi da su samar da madàtsar ruwa wanda zai taimaka wajen noman ranin cikin kwanciyar hankali ba tare da wata matsalaba. Tare kuma da baiwa manoman horo na musammanman akan harkokin noma wanda acewarsa hakan zai taimaka wajen cigaban noma yadda ya kamata.

Ya shawarci matasa da suma su rungumi harkokin noma ko kiwo wanda hakan zai taimaka musu wajen dogaro da kansu.

Labarai Makamanta