Adamawa: Majalisa Ta Amince A Nada Kwamitin Riko A Kananan Hukumomi

Majalisar dokokin Jihar Adamawa ta amincewa Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri da ya nada kwamitin rikon kwaryar shugabannin kananan hukumomi ashirin da daya dake fadin jihar ta Adamawa.

Hakan ya biyo bayan cikar wa’adin zababbun shugabannin kananan hukumomin bayan da hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar ta kasa gudanar da zaben shugabannin kananan hukumomin, wanda ta kudiri aniyar gudanarwa a cikin wannan wata, wanda daga bisani ta ɗaga zaben zuwa illah masha Allah.

Ranar takwas ga watan Disamba na wannan shekara wato wa’adin shugabannin kananan hukumomin zai zo karshen kamar yadda kundin tsarin mulkin jihar ya tanada.

Labarai Makamanta