Adamawa: Kungiyar Manoman Shinkafa Ta Kama Manoma Masu Taurin Bashi

Kungiyar manoman shinkafa a Najeriya RIFAN shiyyar karamar hukumar Yola ta Arewa a jihar Adamawa ta kama manoman Shinkafa dari biyu tare da gurfanar da su a gaban kotu biyo bayan rashin biyan rancen kayayyakin noma da aka basu.

Shugaban kungiyar na karamar hukumar Yola ta Arewa Alhaji Musa Bukar ne ya bayyana haka a zantawarsa da muryar yanci a Yola fadar gwamnatin jahar Adamawa.

Musa Bukar yace daukan matakin haka ya zama wajibi duba da yadda manoman sukayi biris da kayayyakin noma da aka basu wanda a cewarsa sun bi dukkanin hanyoyi da suka dace domin ganin sun biya kayayyakin cikin sauki amman lamarin ya ci tura.

Bukar yace biyan kayayyakin shi zai bada damar ganin cewa an samu cigaba da gudanar da harkokin noma yadda ya kamata kamar yadda gwamnatin tarayya ta kudiri aniyar ganin cewa an bunkasa harkan noma a fadin kasan nan baki daya.

Harwayau Alhaji Musa ya shaidawa muryar yanci cewa cikin mutanen da suka kama tunin ma an tura wasu gidan gyara halinka a yayinda wasu kuma an bada belinsu

Kungiyar RIFAN din dai tana baiwa manoma rancen kayayyakin noma musammanma kananan manoma ƙarƙashin shirin nan na Anchor Browsers wanda gwamnatin tarayya ta kirkiro domin baiwa manoma rance kayayyakin noman wanda ya kama daga kadada daya zuwa biyu.

Wanda kuma rashin biya da dama daga cikin manoma basayi yasa shirin ke samun koma baya.

Labarai Makamanta