Adamawa: Kotu Ta Dawowa Aisha Binani Da Takarar Gwamna A APC


Rahotannin dake shigo mana daga Yola babban birnin Jihar Adamawa na bayyana cewar wata kotun ɗaukaka kara a birnin ba Yola ta tabbatar da Aishatu Dahiru Binani a matsayin halastacciyar ‘yar takarar gwamnan jihar a inuwar jam’iyyar APC.

Kotun da mai shari’a Tanko Yusuf Hassan ya jagoranta ta yi watsi da hukuncin wata kotun tarayya da ya sauke takarar Aishatu Binani, da sanar da cewa APC ba ta da takara a zaɓen 2023.

A lokacin sanar da hukuncinsa, alkalin ya umarci a miƙa sunan Binani ga hukumar zaɓe mai zamanta wato INEC, a matsayin ‘yar takarar gwamnan APC a Adamawa.

Labarai Makamanta