Adamawa: Hatsarin Kwale-Kwale Ya Ci Rayukan Mutane Uku

Rahotanni daga jihar Adamawa sun bayyana cewa wasu mutane uku sun mutu a wani hatsarin Jirgin ruwa da ya afku a jihar Adamawa.

An ruwaito cewa mutanen, wadanda suka kasance maza biyu da mace guda, sun nitse ne a yayinda suke a hanyarsu ta zuwa bikin binne wani ɗan uwansu a yankin karamar hukumar Lamurde.

Da yake tabbatar da lamarin, Shugaban karamar hukumar Lamurde, Burto Williams, ya bayyana lamarin a matsayin abin bakin ciki.

“Hatsarin abin bakin ciki ne da yake bukatar gwamnati ta kawo agaji ga mutanen yankin wadanda ruwa ke yawan yi wa barna.

“Karamar hukumar Lamurde na kokarin samar da kulawar likitoci ga wadanda suka tsira yayin da ƙaramar hukumar za ta dauki nauyin birne mutum uku da suka mutu,” in ji Burto.

Labarai Makamanta