Adamawa: Fintiri Ya Rantsar Da Shugabannin Rikon Kananan Hukumomi

Gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri ya rantsar da Shugabannin riko na kananan hukumomi ashirin da daya dake fadin jihar baki daya.

An dai gudanar da bikin ratsuwarne a dandalin Mahmudu Ribadau dake Yola fadar gwamnati jihar Adamawa.

Da yake rantsar da sabbin shugabannin riko na kananan hukumomi gwamna Fintiri ya kirayi sabbin shugabannin da su maida hankalinsu wajen gudanar da ayyukan cigaban jihar tare da shawartansu da suyi aiki kafada da kafada da hukumomin tsaro wanda hakan zai taimaka wajen wanzar da zaman lafiya.

Ya kuma kirayi magoyan Jam’iyar PDP da su kasance masu hada kansu domin samun cigaban jam’iyar yadda ya kamata.

Shima a jawabinsa shugaban jam’iyar PDP a jihar Adamawa Barista AT Shehu kiran sabbin shugabannin yayi da su hada kai da shugabannin jam’iyar tun daga matakin kananan hukumomi har zuwa jihar.

Da yake magana a madadin sabbin shugabannin Farfesa Abba Tahir wanda shine shugaban karamar hukumar Yola ta kudu ya bayyana godiyarsu ga gwamna bisa wannan mukami da ya basu tare da yin alkawarin gudanar da ayyukansu bil hakki da gaskiya domin samun cigaban jihar baki daya.

Ratsuwar ya gudanane karkashin jagorancin Babban Lauyan jihar kuma kwamishinan shari’an jihar Adamawa Barista Afairemu Jingi.

Labarai Makamanta