Adamawa: Fintiri Ya Nada Shugabannin Rikon Kananan Hukumomi

Gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri ya bayar da sanarwar nadin shuwagabanin rikon kananan hukumomi ashirin da daya dake fadin jihar ta Adamawa.

Hakan na kunshene a cikin wata sanarwa da sakataren watsa labarai na Gwamnan Hunwashi Wanasiko ya fitar wanda aka rabawa manema labarai a Yola.

Nadin shugabanin rikon dai na zuwane bayan da waadin shugabanin kananan hukumomin ya kare tun a ranan 8-12-2021. Wanda kuma majalisar dokokin jihar ta Adamawa ta amincewa gwamnan nada shugabanin riko na kananan hukumomin.

Gwamna Fintiri ya taya wadanda suka samu mukamin murna tare da kiransu da su gudanar da aiyukansu yadda ya kamata.

Nadin shugabanin rikon yazo a dai dai lokacin da hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Adamawa ta bada wa’adin kwanaki casa’in wa jam’iyun siyasar jihar domin shirya zaben shugabanin kananan hukumomin da kansilolinsu.

Labarai Makamanta