Adamawa: Direbobin Keken Napep Sun Koka Akan Tsawwala Rijistar Kekunan Napep

Matuka keken Napep a jahar Adamawa sun koka kan yadda ma aikatar sifirin jahar ta aiyana naira dubu takwas a matsayin yin rijistan keken Napep afadin jahar baki daya.

Shugaban kungiyar matukan keken Napep na M T A a jahar Adamawa Alhaji Bashiru Muhammed Jimeta ne ya baiyayan haka a zantawarsa da manema labarai a yola.

Baahir Muhammed yace sukam basuji dadin abunda ma aikatar sifirin tayiba musammanma yadda take karban kudun fom akan naira dubu daya wanda kuma hakan ya saba dokan yin rijistan maahunan asali basa bada rasitin in ka biya dubu daya.

Don haka nema suke kira ga gwamna da ya kafa kwamitin da zai binciki lamarin wanda acewarsa wanna yunkurine na aikata cin hanci da rashawa. Don haka su basaau yarda da hakaba.

Baahir yace ainihin rijistan keken Napep din anayinsa ne kan naira dubu uku sai kuma kudin da ake biya shekara shekara na naira dubu daya kwatsam zai gashi ma aikatar ta bullo da wani tsarin da basu san da shiba.

Saboda haka dole ne su gabatar da kukansu da kuma bukatarsu domin an dauki magance matsalar baki daya. Ya kuma baiyana cewa in har akabi doka wajen yin rijistan sukam aahirye suke su bada hadin kai wajen yin rijistan ba tare da wata matsalaba.

Harwayau ya kirayi ma aikatar sifirin ta jahar Adamawa da ta bari kowa yaje kungiyar da yakeso yayi rijistan ba wai a ware wasu kungiyoyi da aunan cewa sune za ayi rijistan dasu.

Shima anashi jawabi shugaban kungiyar ta MTA dake karamar hukumar yola ta Arewa Malam Auwal Ihiyaka Ismail yace agaskiya basu dadin abinda ma aikatar sifirin jahar Adamawa ta daukaba. Duba da irin yanayi da ake ciki. Yace aun cimma yarjejeniyar cewa sai a karshen wannan wata na oktoba ne za a fara kama wadanda basuyi rijistaba amma kwatsam sai gashi suna fara kama maahunan da basuyi rijistaba.

Sai dai duk kakarin yan jaridu da sujayi domin jin ta bakin darektan gudanarwan ma aikatar sifirin a jahar Adamawa ya cutura domin yace bai da hurumin yiwa yan jaridu bayani akan lamarin. A yanzu haka dai sama da keken Napep dari ne da aka kama da sunan cewa basuyi rijistaba.

Labarai Makamanta