Adamawa: An Yi Nasarar Damke Dillalin ‘Yan Bindiga

A kokarinta na inganta tsaro harma da kawo karshen ta’addanci a jihar Adamawa, rundunan ‘yan sandan jihar yanzu haka tana tsare da wani matashi bisa zarginsa da sarafan bindigogi a tsakanin jihohin Adamawa da jihar Borno.

Kakakin rundunan yan sandan jihar Adamawa DSP Suleiman Yahaya Nguroje ne ya bayyana haka a wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a Yola.

Sanarwar ta bayyana cewa an kama wanda ake zargin mai suna Shenomano Remos dan shekaru ashirin da biyar da haifuwa, kuma mazaunin kauyen Sheno Belta ne a cikin karamar hukumar Gombi dake jihar Adamawa.

An samu nasaran cika hannu da wanda ake zargin ne a wani shigen binciken hadin gwiwar rundunan ‘yan sandan da mafarauta a cikin garin Gombi inda ya yi fasa kwabrin bindigogin daga karamar hukumar Askira Uba dake jihar Borno zuwa karamar hukumar Gombi a jayhar Adamawa.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Adamawa CP Muhammed Ahmed Barde ya yabawa DPO yankin na Gombi tare dama sauràn Jami’an tsaro bisa namijin kokari da sukayi wajen cafke wanda ake zargin.

Don haka nema kwamishinan ‘yansandan ya tabbatarwa gwamnatin jihar dama al’umma dake fadin jihar cewa rundunàn a kimtse take wajen kare rayuka dama dukiyoyin jama’a a lokaci dama bayan bikin Kirsimeti da ake fuskanta.

Saboda haka nema kwamishina ‘yansandan ya shawarci jama’a da su kasance masu taimakawa rundunan domin ganin ta samu nasaran kawar da aikata laifuka a tsakanin al’umma dama jihar ta Adamawa baki daya.

Harwayau kwamishinan yace zasu cigaba da bincike har sai sun kama wadanda ke da hannu a cikin wannan lamari domin yi musu hukunci.

Labarai Makamanta