Adamawa: An Yi Kiran Hadin Kai Tsakanin Manoma Da Makiyaya

An kirayi Manoma da Makiyaya a fadin Najeriya da su kasance masu hada kansu a koda yaushe domin ganin ba a rinka samun fituntunu a tsakaninsu ba.

Mataimakin shugaban kungiyar Tabbutal Pulaku Jamde jam foundation a jihar Adamawa Alhaji Hassan Ali Soja ne yayi wannan kira a zantawarsa da muryar ‘yanci a Yola.

Alhaji Hassan yace Manoma da Makiyaya su sanifa su ‘yan uwan juna ne saboda haka bai kamata ace ana samun takaddama a tsakaninsu ba, kamata yayi su kaucewa duk abinda zai kawo tashin hankali a tsakaninsu.

Hassan ya kuma shawarci manoma da makiyaya da su kasance masu kai zuciya nesa a duk lokacin da wata matsala ta faru, domin samun cigaba, dama wanzar da zaman lafiya a tsakaninsu.

Ali soja yace a bangaren makiyaya sun daukin matakai daban daban da suka hada hana yaran da basu mallaki hankalinsu ba zuwa kiwo, da kuma hana shaye shaye da dai sauransu, avcewarsa hakan yasa sun samu nasarori wajen samun saukin rikici a tsakanin Manoma da Makiyaya a jihar Adamawa.

Don haka nema yake shawartan manoma da su daina noma akan hanyoyin da Shanu kebi domin zuwa kiwo ko shan ruwa.

Harwayau ya kirayi gwamnatin tarayya dana jihohi da su kafa kwamitin da zai hada da wakilan manoma da makiyaya tun daga matakin kananan hukumomi wanda a cewarsa hakan zai taimaka wajen kawo karshen rikici a tsakanin manoma da makiyaya, a fadin Najeriya baki daya.

Ya kuma yi fatan Allah madaukakin sarki ya kawar da dukkanin kalubalen tsaro a fadin kasan nan baki daya.

Labarai Makamanta