Adamawa: An Yi Kira Ga Mawadata Da Taimakawa Marayu

Àn kira yi al’umma musulmai musammanma mawadata dama wadanda ke rike da madafun iko da su kasance masu maida hankali wajen tallafawa marayu ta fannoni daban daban domin su samu walwala yadda ya kamata.

Shugaban majalisar malamai na kungiyar Izala na jihar Adamawa Mallam Musa Abdullahi ne yayi wannan kira a lokacin da yake jawabi a wurin musabakar karatun Alqur’ani mai girma wanda makarantar Marayu ta Annur ta shirya a Yola.

Malam Musa yace taimakawa Marayu da bude makarantu zai basu damar samun ilimi yadda ya kamata domin haka ya kamata al’umma musulmai su maida hankali wajen taimakawa Marayu don taimaka musu yana da matukar muhimmanci anan duniya da ranar gobe kiyama.

Shima anashi jawabi Alhaji Lawan wanda shine ya assasa Makarantar Marayu ta Annur kira yayi wa al’umma musulmai da a hada hannu wajen samun cigaban makarantar domin ganin marayun sun samu ingantaccen ilimi domin samun cigaba a rayuwarsu a bangarori dabàn daban.

Ya kuma yabawa malamai dama kwamitin makarantar bisa jajircewa da sadaukar da kai wajen ganin dalibai Marayun sun samu ilimi yadda ya kamata.

Tunda farko a jawabinsa na maraba shugaban kwamitin makarantar Alhaji Baba Iyali ya shawarci Al’umma musulmai da su kasance masu baiwa makarantar hadin kai da goyon baya domin ganin an samu nasaran ilimantar da marayun ba tare da matsala ba.

Da yake gabatar da nasiha sakataren majalisar malamai Malam Salihu Dauda shawartan al’umma musulmi yayi da su kasance masu taimakawa marayun ta fannoni daban daban da suka hada da kayayyakin karatu, abinci, tufafin sawa, da dai sauransu.

Wasu daga cikin daliban da suka samu nasara a musabakan sun bayyanawa muryar ‘yanci farin cikinsu dangane da wannan musabaka da aka shirya musu wanda hakan zai basu damar kara kwazo wurin karatun al qur’ani mai girma. Dama sauran karatuttuka.

Akalla dalibai talatin ne dai suka shiga musabakar karatun Al qur’ani mai girma. Wanda kuma dalibai ashirin da hudu suka samu nasarar samun kyaututtuka.

An kuma gabatar da Addu’o’i na musamman domin neman taimakon Allah madaukakin sarki wajen kawo karshen matsalar tsaro a fadin Najeriya baki daya.

Labarai Makamanta