Adamawa: An Yi Gangamin Wayar Da Kan Manoma Da Makiyaya

Domin ganin an samar da zaman lafiya a tsakanin manoma da makiyaya a jihar Adamawa an shirya gangamin wayarwa manoma da makiyayan kai dangane da muhimancin zaman lafiya a tsakaninsu.

An gudanar da gangamin ne karkashin MESSCOP wanda aka gudanar a garin Tambo dake cikin karamar hukumar Girei a jihar Adamawa.

Da yake jawabi a wurin gangamin Keansline Maxwell wanda shine sakataren jungiyar ta MESSCOP yaja hankalin makiyayan da manoman da su kasance masu kai zuciya nesa da kuma hakuri a koda yaushe wanda a cewarsa hakan zai taimaka wajen cigaban zaman lafiya a tsakaninsu.

Ya kuma kirayi gwamnati dama sarakunan gargajiya da su kasance masu maida hankali a bangaren Manoma da makiyayan domin ganin an kaucewa duk abinda zai kawo karshen tashin hankali a tsakaninsu baki daya.

Shima a jawabinsa Malam Ardo Balel Sumo wanda ya wakilci makiyayan a wurin taron ya bayyana farin cikinsa dangane da wannan taro wanda a cewarsa yin taron yana da muhimmanci domin za a dauki matakin dakile duk wata fitina a tsakanin makiyayan da manoma.

Ya kuma tabbatar da cewa za suyi dukkanin abinda ya kamata domin ganin an magance matsaloli dake faruwa a tsakaninsu

Anashi bangaren Sondagi Ngari wanda shi ya wakilci manoma shima yabawa yayi dangane da shirya wannna taro inda yace shirya irin wanan taro zai taimaka wajen kawo karshen matsalar baki daya.

Ya kuma kirayi yan Najeriya da su cigaba dayin addu’a domin neman taimakon Allah madaukakin sarki wajen kawo karshen duk wasu kalubalen tsaro a fadin kasan nan baki daya.

Labarai Makamanta