Adamawa: An Shirya Wa Dalibai Mata Hanyar Kula Da Lafiya

Domin ganin an dauki matakin kariya daga cututtuka musammanma a tsakanin dalibai hakan yasa aka shiryawa dalibai mata taron gangamin wayarwa da kai dangane da yadda zasu kula da lafiyarsu.

Taron gangamin wanda ya gudana karkashin jagorancin Kungiyar mata na wanzar da zaman lafiya tare da hadin gwiwar Dan Lawan Adamawa Alhaji Sadiq Umar Daware wanda akayi a Yola.

A jawabinta Uwar gidan gwamnan jihar Adamawa Hajiya Lami Umar Fintiri wanda kwamishiniyar ilimin jahar Adamawa Wilbina Jackson ta wakilta ta kirayi daliban da sukasance masu kula da lafiyarsu a koda yaushe domin kaucewa kamuwa da cututtuka.

Ta kuma shawarce su tare da su rinka tuntuban masana kiwon lafiya a duk lokacin da zasuyi amfani da kayayyakin kiwon lafiya ko kuma sunji abinda basu ganeba a jikinsu domin samar da wadataccen lafiya.

Itama a jawabinta Hajiya Sa’adatu Gidado kiran iyaye ta yi da su maida hankali wajen baiwa yaransu ilimi a koda yaushe domin samun cigaban ilimi dama samar da zaman lafiya a tsakanin al’umma baki daya.

Da yake nashi jawabi a wurin taron Dan Lawan Adamawa Alhaji Sadiq Umar Daware yace kula da lafiya abune da yake da mutakan muhimmanci don haka dolene a dauki dukkanin matakai da ya dace domin kula dama kariya daga cututtuka.

Don haka nema yace samarwa daliban ilimi zai taimaka wajen bunkasa kiwon lafiya harma da samar da zaman lafiya a tsakanin Jama a baki daya.

Halima Ibrahim wanda tayi magana a madadin daliban ta bayyana farin cikinta dangane da wannan taro da aka shirya musu wanda a cewarta yazo a dai dai lokacin da ya dace.

Sama da ɗalibai dari shida ne dai suka halarci taron tare da rarraba musu kayayyakin kula da lafiya da suka hada da sabulai audugar mata da dai sauransu.

Labarai Makamanta