Site icon Muryar 'Yanci – Labaru, Siyasa, Tsaro, Lafiya, Ilimi…

Adamawa: An Shawarci Musulmi Da Rungumar Karatun Alkur’ani

An shawarci al umma musulmai da su kasance masu kara himma wajen karanta Al qur ani mai girma domin samun cigaban addinin musulunci dama samun hadin kan musulmai baki daya.

Mallam Baahir Ali shugaban alkalin alkalai a wajen gasan karatun Alqur ani mai girma ne ya baiyana haka a lokacin yake jawabi a wurin bude gasan karatun Al qur ani mai girma a yola.

Gasan wanda zai gudana karkaahin RABIDH wanda kungiyar tallafawa mata musulmai a Najeriya wato IMWON shiyar jahar Adamawa ta shirya a yola.

Gasar wanda za ayi a tsakani dalube mata zalla wanda kuma ahine karo na farko da za a gudanar a jahar Adamawa, wanda ya samu halartan dalube mata daga kananan hukumomi aahirin da daya dake fadin jahar Adamawa.

Mallam Bashir ya kuma kirayi iyaye da su maida hankali wajen tura yaransu makarantu domin samun cigaban addinin a tsakanin al umma musulmai.

Shima a jawabinsa ko odinaton kungiya ta RABIDAH a jahar Adamawa Mallam Yahatu Imam shawartan al umma musulmai yayi da sukasance masu maida hankali wajen yin adu o i domin taimakon Allah ma daukakin sarki ya kawo karshen kalubalen tsaro da ake fama daahi a fadin kasan nan baki daya.

Tunda farko a jawabinta shugabar kungiyar tallafawa mata musulmai a Najeriya shiyar jahar Adamawa Hajiya Asma u Abubakar ta baiyana farin cikinta tare da jin dadinta dangane da ahirya wannan gasa na karatun al qur ani mai girma wanda kuma shine karo na farko a jahar Adamawa.

Hakimin Jimeta kuma dan isan Adamawa Muhammadu Inuwa Baba Paris wanda maijimillan anguwar yelwa Ya u Dahiru ya wakilta wanda kuma shinema ya kaddamar da bude gasan karatun Al qur ani mai girma.

Ya kuma shawarci Matasa da suma su maida hankali wajen karatun addinin musulunci da ma adu o i domin samar da zaman lafiya a jahar dama kasa baki daya.

Dalube da suka fito daga kananan hukumomi aahirin da daya ne dai suka shiga gasar na wannan ahekara ta dub biyu da aahirin da daya.

Exit mobile version