Adamawa: An Shawarci Musulmi Da Bude Makarantun Islamiyya

A wani mataki na inganta karatun addinin musulunci an kirayi al’umma Musulmi da su maida hankali wajen bude makarantun islamiyoyi tare kuma da ingantasu domin samun cigaban addinin musulunci.

Shugaban majalisar makarantun islamiyoyi a jihar Adamawa Mallam Muktar Dayyib ne yayi wannan kira a zantawarsa da manema labarai a Yola.

Mallam Muktar ya kuma ja hankalin iyaye da malamai da su kasance masu hada kansu domin yin aiki kafada da kafada wanda a cewarsa hakan zai karawa yaran kwarin gwiwa ta maida hankali akan karatunsu yadda ya kamata.

Da wannan ne yake kira ga malamai da su kasance masu fadakar da al umma Musulmai muhimmancin karatun addinin musulunci kasancewa yana da muhimmanci a duniya da lahira.

Ya kuma shawaci matasa da su kasance suna bada tasu muhimmiyar gudumawa wajen cigaban addinin musulunci domin samun tsira ranan gobe kiyama.

Mallam Muktar Dayyib yace samar da makarantun islamiyoyi zai taimaka wajen inganta ilimi a tsakanin yara da kuma samar da inganceccen tarbiya a tsakanin dalibai yadda ya kamata.

Labarai Makamanta