Adamawa: An Shawarci Musulmi Da Ayyukan Hadin Kai A Bikin Maulidi

An kirayi al’umma musulmai suyi amfanin da wannan lokaci na bukukuwar maulidi wajen gudanar da ayyukan hadin kan al umma da kuma nunawa juna kauna domin samar da zaman lafiya dama cigaban kasa baki daya.

Alhaji Adamu Jingi ne yayi wannan kira a lokacin da yake zantawa da muryar yanci kan bikin na maulidi a yola fadar gwamnatin jahar ta Adamawa.

Alhaji Adamu yace hadin kai a tsakanin al umma musulmai yana da mutukan muhimmanci wanda acewarsa hakan zai taimaka wajen cigaban addinin musulunci yadda yakamata.

Jingi ya kuma shawarci al umma musulmai da suyi koyi da halayen manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi domin samun zaman lafiya mai daurewa a fadin kasanan baki daya.

Adamu Jingi ya kuma nuna takaicinsa dangane da hari da yan bindiga suka kai a kasuwar Goronyo wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane da dama tare da jikkata wasu da dama.

Don hakanema yake mika ta aziyarsa ga gwamnatin jahar karkashin Aminu Tambuwal dama mai alfarma sarkin musulmai Alhaji Abubakar Sa ad harma da al ummar jahar baki daya bisa rashin yan kasuwa da akayi tare dayin adu ar Allah ya baiwa wadanda suka jikkata lafiya.

Ya kuma kirayi gwamnatin tarayya dana jahar da su kara kaimi wajen inganta tsaro a jahar dama kasa baki daya domin ganin an kawo karshen dukkanin kalubalen tsaro a fadin kasan nan baki daya.

Ya kuma yaba da yandda hukumomin tsaro ke gudanar da aiyukansu domin kawo karshen matsalar tsaro baki daya.

Labarai Makamanta