Adamawa: An Shawarci Matasa Su Tsunduma Cikin Siyasa

An shawarci matasa a Najeriya da su kasance masu shiga a dama dasu a cikin siyasa kasancewa suma suna da rawan da zasu iya takawa wajen cigaban kasa harma da samar da zaman lafiya.

Shugaban shugabannin matasa na jam iyar PDP a jihar Adamawa Abdulrahman Musa ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Yola.

Abdulrahman Musa yace Matasa su sani fa sune kashin bayan al’umma don su maida hankalinsu wajen gudanar da ayyukan cigaban kasa harma da wanzar da zaman lafiya.

Abdulrahman ya kuma kirayi matasan da su nesanta kansu daga aikata duk abinda zai zubar musu da mutuncinsu a idon al’umma tare kuma da kaucewa tu’ammali da miyagun kwayoyi, bangan siyasa da dai sauransu.

Harwayau ya kirayi iyaye da cewa suma suna da muhimmiyar rawa da zasu iya takawa wajen inganta rayuwar matasan kasancewa suna tare dasu tun suna yara har zuwa girmansu.

Don haka nema yake shawartan iyayen da su kasance masu yiwa yaransu addu’a a koda yaushe wanda acewar sa hakan zai taimakawa wajen cigaban yaran yadda ya kamata.

Ya kuma kirayi gwamnatoci a dukkanin matakai da su kasance masu ba matasan mukamai domin suma su bada tasu gudamawan wajen bunkasa cigàban kasan baki daya.

Labarai Makamanta